Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya yi kira ga kasashe mahalarta taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, da su yi hadin gwiwa wajen gina tattalin arzikin duniya, wanda zai zamo mai amfani ga dukkanin sassa.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin taron kungiyar dake gudana yanzu haka a birnin Hamburg na Jamus, ya ce akwai bukatar inganta harkokin cinikayyar kasashe ba tare da sanya shingaye ba.
A bana dai taron kungiyar G20 zai guda ne tsakanin ranekun 7 zuwa 8 ga watan nan na Yuli, an kuma yiwa taron taken "daidaita sassan duniya masu da alaka da juna".(Saminu Alhassan)