in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Teresa May
2017-07-08 13:20:50 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministar kasar Birtaniya Teresa May jiya Jumma'a, a birnin Hamburg na kasar Jamus.

Yayin ganawarsu, Xi Jinping ya ce, wani tushe ga yunkurin raya huldar dake tsakanin Sin da Birtaniya shi ne, karfafa aminta da juna, musamman ma ta fuskar wasu manyan tsare-tsaren kasashen 2.

A cewar shugaban kasar Sin, kamata ya yi, bangarorin 2 su tsaya kan girmama juna, da tabbatar da daidaito tsakaninsu, da lura da babbar moriya da manyan batutuwan da ke janyo hankulan kasashen yadda ya kamata. Sai dai ya ce, domin cimma wannan muradi, ya kamata a kara hadin gwiwa tsakanin kasashen 2.

A cewar Xi, ya kamata a dauki matakai bisa shawarar "ziri daya da hanya daya ", inda za a gudanar da shirin raya kasa ta kasar Sin daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, da shirin samar da kayayyaki masu inganci nan da shekarar 2025 na kasar Sin, da manufar raya sana'o'in zamani ta kasar Birtaniya, da shirin kafa cibiyar tattalin arziki a arewacin yankin Ingila, da dai sauran manyan tsare-tsaren kasashen 2, tare da zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskokin hada-hadar kudi da aikin samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya.

A nata bangaren, firaminista Teresa May ta ce, kasarta tana so a yi amfani da tsarin tattaunawa tsakanin manyan shugabannin kasashen 2, don kara musayar ra'ayi tare da hadin gwiwa, a fannonin cinikayya, zuba jari, al'adu, da harkar tsaro, da dai makamantansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China