Xi Jinping ya bukaci Japan ta dauki darasi daga tarihi domin samun makoma mai kyau, inda ya ce ya kamata Shinzo Abe ya kawar da duk wani tarnaki domin kyautata huldar dake tsakaninsu.
Shugaban na Sin ya kuma nemi Japan ta dauki ingantattun matakan da za su tabbatar da zaman lafiya da kawance tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau, shugaba Xi wanda ya ce kasarsa na maraba da Japan ta shiga shawarar 'ziri daya da hanya daya', ya ce babu batun yarjejeniya game da abun da ya wuce da kuma yankin Taiwan, yana mai bukatar Japan ta daraja furucin da ta yi.
A nasa bangaren, Firaministan Japan Shinzo Abe ya ce a shirye yake ya yi hasashen makoma mai kyau tare da inganta huldarsa da kasar Sin, inda ya yi alkawarin ba zai sauya matsaya game da yankin Taiwan na kasar Sin ba.
Bugu da kari, ya yi fatan cewa za a inganta musayar ra'ayi da harkokin cinikayya da hada-hadar kudi da yawon bude ido tsakanin Japan da kasar Sin (Fa'iza Mustapha)