A yayin bikin bude taron, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, nuna goyon baya kan tsarin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban wanda aka yi kwaskwarima da kuma samun kyautatuwa, shi ne nauyin dake gaban MDD. Mutanen duniya za su iya samun ci gaba tare ta hanyar daukar matakan da za su dace da halin da muke ciki cikin hadin gwiwa.
Ban da haka kuma, ya tattauna kan muhimmancin fuskantar matsalar sauyin yanayi da kuma yin amfani da sabbin fasahohi, kana ya nuna damuwarsa matuka kan yaduwar ra'ayoyin ta'addanci da makaman nukiliya a nan duniya.
A nata bangare kuma, shugabar babban taron MDD karo na 73 Maria Fernanda Espinosa ta yi kira da a gina MDD ta yadda za ta kula da kowa da kowa, kuma tsarin hadin gwiwa shi ne hanyar daya kadai da za a iya yin amfani da ita wajen warware dukkanin matsalolin da bil Adama suke gamuwa da su. (Maryam)