Antonio Guterres ne ya jagoranci jami'an majalisar da ma'aikata da iyalan da suka yi jawabi a babban zauren MDD yayin wani taro da aka yi don tunawa da Kofi Annan da ya taba samun lambar yabo kan zaman lafiya, wanda ya rasu a ranar 18 ga watan Augusta a birnin Geneva, bayan gajeriyar rashin lafiya.
Sakatare Janar din ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kwarai kuma na kowa, kana wayayye kuma mai hangen nesa, wanda ya kasance jajirtacce wajen kiyaye dokokin MDD.
Antonio Guteress wanda Kofi Annan ya nada matsayin shuguban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a shekarar 2005, ya kara da cewa, a wasu lokuta mutane kan shagala da ganinsa a wuri ba tare da sun tuna cewa fadakar da su ake ba.
Ya ce tsawon wa'adin aikinsa, Kofi Annan ya yi ta kira gare su, da kada su zama 'yan kallo a rayuwa, inda ya bukaci su yi adawa da nuna bambanci da rashin imani da zub da jini. (Fa'iza Mustapha)