in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yabawa shirin yaki da yunwa
2018-09-24 13:43:04 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yabawa da shirin yaki da yunwa da bankin duniya da Majalisar suka gabatar, wanda ya kasance wani sabon mataki na karewa da taimakawa yaki da yunwa.

Antonio Guterres, ya bayyana yayin kaddamar da shirin a hedkwatar MDD dake binin New York cewa, an samu nasarar gabatar da shirin ne bisa hadin gwiwa masu ruwa da tsaki daban-daban da suka hada da hukumomin bada agajin jin kai da kamfanonin masu hidimar samar da fasahohi da cibiyoyin ilimi da kamfanonin inshora da dai sauransu.

Ya ce shirin, zai ba da dama wajen tantance hakikanin halin da ake ciki game da wadatar abinci, tare da zaburar da masu bada gudunmuwa da hukumomin jin kai da za su ceto rayuka da kare jama'a daga ci gaba da kasancewa cikin halin matsi.

Har ila yau, shirin zai yi amfani da fasahohi ciki har da na'urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam, domin gano alakar dake tsakanin haddura daban- daban.

A cewar Sakatare Janar na MDD, karfafa hadin gwiwa zai taimakawa masu bada gudunmuwa da kasashen da abun ya shafa da hukumomin kasa da kasa, wajen cike gibin kudi da ake fuskanta a baki dayan ayyukan bada agajin jin kai, tun daga daukar matakan kariya har zuwa shirin tunkarar bukatun gaggawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China