in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya lashi takobin hana masu safarar miyagun kwayoyi samun mafaka
2018-09-25 09:36:23 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce dole ne a yi kokarin hana masu fasa kaurin miyagun kwayoyi samun mafaka.

Da yake jawabi ga wani taron manyan jami'ai da aka yi wa lakabi da "kira ga al'ummar duniya don daukar mataki kan matsalar miyagun kwayoyi a duniya", Sakatare Janar din ya ce matsalar da ake ci ciki game da miyagun kwayoyi abun tada hankali ne.

Da yake bayyana matsalar a matsayin wanda ka iya samun kowa a kowane lokaci, ya ce daukar mataki a yanzu hakki ne da ya rataya a kan kowa.

Ya ce a shekarun baya-bayan nan, wasu mutane miliyan 31 a fadin duniya na bukatar kulawa ta lafiya saboda shan kwayoyi fiye da kima, inda ya ce wasu mutane 450,000 kuma na mutuwa duk shekara saboda shan kwayoyin fiye da kima ko kuma wasu matsalolin lafiya dake da alaka da shan kwayoyin.

Domin kawo karshen wannan matsalar, Antonio Guterres ya ce dole ne a yi kokarin yaki da masu safarar kwayoyi da wadanda ke amfana daga halin zullumi da mutane kan shiga, tare kuma da tabbatar da wadanda ke bukatar kulawa sun samu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China