in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU, EU, UN sun lashi takobin inaganta dangantakar kasa da kasa
2018-09-25 10:20:20 cri
Tarayyar Afrika AU da Tarayyar Turai EU da kuma MDD, sun jadadda kudurinsu na inganta tsarin hulda da dangantaka tsakanin kasa da kasa.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar jiya, bayan taron da bangarorin 3 saba yi duk shekara, sun bayyana aniyarsu ta daukar matakin karfafa hadin kai wajen magance kalubalen da ake fuskanta a duniya bisa hadin gwiwar kasa da kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, AU da EU da MDD, sun yi niyyar inganta hadin gwiwarsu a bangarorin siyasa da tattalin arziki da ayyuka kan mabanbantan batutuwa, musamman wadanda suka jibanci zaman lafiya da tsaro da aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ajandar AU ta 2063 da samar ci gaba mai dorewa na bai daya da kare hakkin bil adama da sauyin yanayi da kuma mara baya ga aiwatar da sauye-sauyen AU da MDD.

Hukummomin 3, za kuma su ci gaba da aiki tare, wajen tallafawa kasashen yankin Sahel da sauran wuraren masu fama da rikici kamar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Somalia da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Libya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China