Mr. Guterres na wannan tsokaci ne, a jawabin da ya gabatar, albarkacin taron wanzar da zaman lafiya da aka yiwa lakabi da A4P, a wani bangare na taron kolin MDD karo na 73 dake gudana yanzu haka a helkwatar MDDr dake birnin New York.
Ya ce "kare fararen hula aiki ne mai matukar muhimmanci da ya rataya a wuyan jami'an wanzar da zaman lafiya. Kuma ba za mu taba mantawa da mummunan sakamakon dake biyo bayan gazawar mu ba".
Daga nan sai ya jaddada kira ga sassan masu ruwa da tsaki na yankuna da kasashe, da su ci gaba da fadada hadin gwiwa da juna, matakin da a cewar sa, zai taimaka matuka ga cimma nasarar matakan siyasa, da na gudanarwa, masu nasaba da ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Mr. Guterres ya kuma jinjinawa jami'an wanzar da zaman lafiya masu aiki a nahiyar Afirka, yana mai cewa "Idan akwai bukatar yaki da ta'addanci, ko wanzar da zaman lafiya, dakarun dake aiki a nahiyar, ciki hadda wadanda kungiyar AU ke turawa, na taka rawar gani yadda ya kamata. Don haka ya yi kira ga kasashe mambonin MDD, da su marawa irin wadannan ayyuka baya, ta hanyar samar da kudade isassu kuma a kan lokaci.(Saminu Alhassan)