Wakilan wadanda suka kunshi shugabannin kasashe da manyan kusoshin gwamnatoci, sun bayyana hakan ne jiya Litinin, yayin taron tattauna batutuwa da suka shafi zaman lafiya, wanda aka sadaukar ga Nelson Mandela, sun kuma amince da wani kuduri na farko yayin taron na bana, mai take "Zage damtse ga martaba juna, da juriya, tare da fahimtar juna, da cimma maslaha tsakanin sassa daban daban."
Har ila yau, wakilan kasashen sun jaddada muhimmancin cimma nasarar ajandar wanzar da ci gaba ta nan da shekarar 2030, suna masu cewa za su tsaya tsayin daka wajen cimma nasarar sassan ta 3, da suka hada da raya tattalin arziki, da kyautata zamantakewa da kare muhalli, a yanayin daidaito da hade dukkanin sassa.
A tsokacinsa game da batun, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce rayuwar Mandela ta alamta dukkanin kudurorin MDD, duba da yadda ya sadaukar da rayuwar sa ga hidimta wa al'umma.
Mandela ya kasance lauya, wanda ya yi zaman gidan yari, kana ya zamo mai shiga tsakani, mai kuma wanzar da zaman lafiya. Kana tsohon shugaban kasa wanda daga karshe ya zamo dattijo da ake martabawa.
A watan Disambar shekarar 2017, mambobin MDD suka yanke shawarar gudanar da taro na farko na MDD game da zaman lafiya, a matsayin bikin cikar Mandela shekaru 100 da haihuwa. (Saminu Hassan)