Wang Qun Ya ce, an kara wasu sabbin matakai masu amfani cikin kudurin, inda aka yi maraba da ci gaban da aka samu kan batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa, tare kuma da nuna goyon baya ga harkokin diflomasiyya. Ya ce kudurin na da muhimmanci kwarai da gaske, musamman ma a lokacin da ake fama da matsalar warware batun nukiliyar zirin Koriya ta hanyar diflomasiyya.
Wang Qun ya ce, cikin kudurin, an yi maraba da shawarwarin da aka yi a kwanakin baya, tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu, da Koriya ta Arewa da kasar Sin, da kuma Arewar da Amurka. Kuma abin farin ciki shi ne, sanarwar da Koriya ta Arewa ta fitar na dakatar da gwajin nukiliya da kuma lalata cibiyar gwajin, inda ta kuma sa kaimi ga bangarori daban daban da abin ya shafa, wajen cika alkawarin da suka yi cikin yarjejeniyoyin "Sanarwar Panmunjom" da aka kulla a bana, da kuma "Sanarwar Pyongyang ta watan Satumaba" da aka kulla tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu.
Haka zalika ya ce, kasar Sin ta halarci ayyukan shawarwari kan tsara wannan kuduri, tare da bada shawarwari masu amfani da dama, wadanda suka bada gudummawa matuka ga zartaswar kudurin. (Maryam)