Shugabannin Koriya ta kudu da ta Arewa sun sanya hannu kan wata muhimmiyar takarda
A yau Laraba ne shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da takwaransa na kasar Koriya ta kudu Moon Jae-in suka sanya hannu kan wata muhimmiyar takarda bayan ganawarsu ta keke da keke karo na biyu a birnin Pyongyang. Sai dai ba a yi wani karin haske game da wannan muhimmiyar takarda ba.
Baya ga jagororin biyu, shugabannin tsaron kasashen biyu ma sun sanya kan wata yarjejeniya game da rage ayyukan soja a zirin na Koriya. (Ibrahim)