in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Koriya ta arewa ya tabbatar da daukar matakan kammala kawar da makaman nukiliya
2018-09-06 10:57:59 cri
Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un ya sake nanata aniyarsa na tabbbatar da kawar da shirin kera makaman nukiliya a zirin Koriya, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Koriya ta kudu ne ya tabbatar da hakan bayan da ya ziyarci Pyongyang a kwanakin baya.

Chung Eui-yong, babban mashawarci ga shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jae-in wanda ya jagoranci tawagar musamman mai mambobi 5, ya bayyana a taron manema labarai cewa shugaban Koriya ta arewa ya tabbatar da aniyarsa na kawo karshen takaddama kan makaman nukiliyar a zirin Koriya, kuma ya bayyana aniyarsa na yin aiki kafada da kafada da Koriya ta kudu da kuma Amurka game da shirin kawar da makaman nukiliyar.

Chung da sauran wakilan tawagar 4 sun gana da Kim Jong Un a Pyongyang a lokacin ziyararsu ta wuni guda a matsayin tawagar musamman, inda suka gabatar da sakon wasikar Moon ga jagoran na Koriya ta arewa.

Chung ya ce Koriyoyin biyu sun amince za su gudanar da taron kolin Moon-Kim karo na uku a babban birnin Koriya ta arewa tsakanin ranakun 18 zuwa 20 ga watan Satumba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China