A wajen wani taro kan batun nukiliya na zirin Koriya da kwamitin sulhun MDD ya shirya, jakada Ma ya ce, Sin na goyon-bayan Amurka da Koriya ta Arewa su daidaita matsalar makamashin nukiliya na zirin Koriya ta hanyar yin shawarwari, haka kuma Sin na fatan kasashen biyu za su tabbatar da nasarorin da aka samu a wajen shawarwarinsu. Ma ya ce, kasar Sin na goyon-bayan kara yin mu'amala da shawarwari tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu, tana kuma fatan shugabannin kasashen biyu za su yi shawarwari cikin nasara a Pyongyang.
Har wa yau, Ma ya ce, kasar Sin ta yaba matuka ga kokarin da Koriya ta Arewa ta yi wajen kawar da makaman nukiliyarta gami da tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriyar. (Murtala Zhang)