Bayan saukar Shugaba Moon, shugabannin sun yi musabaha tare da rungumar juna. Wannan shi ne ganawa ta farko tsakanin shugabannin kasashen biyu a Pyongyang, babban birnin Koriya ta arewa, cikin shekaru 11.
Kamfanin dillancin labarai na KCNA, ya ce taron na Pyongyang, na da nufin aiwatar da yarjejeniyar Panmunjon da aka cimma bayan ganawar shugabannin ta farko a watan Afrilun bana.
KCNA ya kara da cewa, taron zai samar da muhimmiyar dama ta kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen tare da shiga sabon shafin tarihi. (Fa'iza Mustapha)