'Yan jaridun sun nemi jin ra'ayin Wang Yi, game da tsokacin da wasu kasashe da bangarori suka yi a kwanakin baya, na cewa kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin da wasu kasashe suka yi, ciki har da kasar Dominican, ya sauya halin da lardin Taiwan ke ciki, kuma zai haddasa illa ga kiyaye yanayin zaman lafiya da ci gaban lardin.
Da yake amsa tambayar, Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce daya tilo a duniya, kuma lardin Taiwan, daya ne daga cikin yankunan kasar, don haka, ba za a iya raba su ba. Ya ce gamayyar kasa da kasa sun riga sun cimma matsaya guda kan wannan batu. Kuma kulla dangantakar diflomasiyya da Kasar Dominican da wasu kasashen duniya suka yi da kasar Sin, ya dace halin da ake ciki yanzu, kuma abu ne mai kyau da ya dace da moriyar al'ummomi da kasar Dominican.
Dangane da batun "sauya halin da lardin Taiwan yake ciki" kuwa, ya ce ya kamata a halin yanzu, jam'iyyar Min Jin, mai mulkin lardin Taiwa, ta ba ta tsayar da yunkurin raba lardin daga kasar Sin ba, kuma ayyukan da ta ke yi, sun bata huldar dake tsakanin lardin Taiwan da babban yankin kasar Sin, da kuma halin da lardin Taiwan yake ciki, wato na kasancewarsa lardin kasar Sin, ba wata kasa ta daban ba. (Maryam)