Wang ya ce, taron kolin ya kasance taron diplomasiyya ne mafi kasaita Sin ta taba karbar bakuncinsa. A karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping, Sin da kasashen Afirka sun yi hadin kai da sahihiyar zuciya, har ma sun cimma jerin nasarori masu ma'ana. Kaza lika taron kolin ya kasance alama ta karfafa hadin kai, da neman ci gaba tare a tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Bilkisu)