Wang Yi, ya ce ya kamata al'ummomin duniya su kiyaye tsarin huldar kasa da kasa bisa manufofi da ka'idojin da MDD ta gindaya, tare da kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya ta kowacce fuska kuma a bayyane, sannan bisa daidaito da adalci ta yadda kowa zai mora.
Ya kuma yi kira da a yi adawa da ra'ayi na kashin kai da kariyar cinikayya, tare da kare dokokin kasa da kasa da muradun jama'ar duniya.
A nata bangaren, Espinosa Garces, ta yabawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen goyon bayan huldar kasa da kasa da ayyukan MDD.
Ta kuma yabawa shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya' inda ta bayyana ta a matsayin kyakkyawar gudunmuwar da za ta bunkasa ci gaban duniya, ta na mai cewa, za ta ci gaba da marawa shawarar baya, kana ta na sa ran kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)