in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana ra'ayoyinsa kan batun gyara tsarin cinikin duniya
2018-09-14 11:29:02 cri

Jiya Alhamis, bayan ganawarsu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi tare da takwaransa na kasar Faransa sun gana da 'yan jaridu a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wang Yi ya ce, tsarin cinikin duniya na halin yanzu yana fuskantar wasu kalubaloli, a ganin kasar Sin, ya kamata a kiyaye ra'ayin yin ciniki cikin 'yanci, yayin da a karfafa tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. A sa'i daya kuma, tsarin cinikin duniya da ake yin amfani da shi a halin yanzu ba marar aibi ba ne, kasar Sin tana goyon bayan kyautata tsarin ciniki bisa ka'idojin kungiyar WTO, domin tsara wani sabon tsari mai cike da adalci, da inganci kuma mai dacewa.

Dangane da yadda za a aiwatar da kwaskwarima kan wannan aiki, Mr. Wang ya ce, ya kamata mu tsaya tsayin daka kan ka'idoji guda uku, na farko, mu kiyaye tushen ka'idoji na kungiyar WTO. Na biyu kuwa shi ne, mu kiyaye moriyar kasashe masu tasowa yadda ya kamata. A karshe, ya kamata mu saurari ra'ayoyin bangarori daban daban domin neman cimma daidaituwar baki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China