in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya ce kasarsa ba za ta yarda a nuna fin karfin tattalin arziki ba
2018-07-31 10:20:10 cri
Jiya Litinin, a Beijing, memba a majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaransa na kasar Birtaniya Jeremy Hunt sun halarci shawarwarin kasashen biyu karo na tara bisa manyan tsare-tsare, inda Wang ya bayyanawa kafofin watsa labarai matsayin gwamnatin kasar game da takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka.

Wang Yi ya ce, gudanar da cinikayya cikin 'yanci ra'ayi daya ne da kasa da kasa suka cimma, kana, ci gaban tarihi ne da ba za'a iya hanawa ba. ya na mai cewa, kasar Sin ta dade tana kare tsarin yin cinikayya ba tare da kafa wani shinge ba.

Wang ya kara da cewa, mu'amalar kasa da kasa na kama da mu'amala tsakanin dan Adam, wato ya kamata a nunawa juna aminci da gaskiya, tare kuma da girmama ka'idoji.

Wang ya nuna cewa, na farko, kasancewar rashin daidaiton cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba laifin kasar Sin ba ne. Na biyu, samun rarar kudin cinikayya ko gibi, ba ma'auni ne da zai iya tantance gaskiya ba. Na uku, Amurka ita ce ta kaddamar da yakin cinikayya tun farko ba kasar Sin ba. Na hudu, kaddamar da tankiyar cinikayya da Amurka ta yi ba ya bisa doka.

Wang ya kara da cewa, har kullum kofar kasar Sin a bude take wajen yin shawarwari da Amurka, amma ya zama dole yin shawarwarin ya zama bisa tushen mutunta juna da nunawa juna adalci, kana kuma, matsa lamba da yin barazana daga bangare daya ba zai yi nasara ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China