Game da tambayar da 'yan jarida suka yi masa na cewa, yadda Sin da Birtaniya za su yi kokarin aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' tare, Mista Wang ya ce, Birtaniya babbar aminiyar hadin-gwiwa ce ga kasar Sin wajen aiwatar da shawarar, kana, ita ce kasa ta farko dake yammacin duniya wadda ta nemi izinin shiga cikin bankin zuba jari na inganta ababen more rayuwar jama'ar Asiya ko kuma AIIB a takaice, kuma kasar yammacin duniya ta farko da ta sa hannu kan ka'idojin tanadin kudi kan shawarar 'ziri daya da hanya daya', haka zalika ita ce ta farko da ta zuba kudi a cikin asusun musamman na bankin AIIB.
Wang Yi ya kuma ce, shi da Hunt sun cimma matsaya daya kan kara hadin-gwiwa tsakanin kasashensu a fannonin da suka shafi harkokin kudi da doka da kuma yin kirkire-kirkire. Ya ce Sin na maraba da kamfanonin Birtaniya don su nuna kwazonsu a fannonin kudi da doka, da kuma kara hada kai da kasar Sin wajen aiwatar da ayyukan da suka jibanci shawarar 'ziri daya da hanya'.(Murtala Zhang)