in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Singapore sun amince su kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama da kuma cinikayya maras shinge
2018-08-02 12:32:23 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, wanda ke ziyara a Singapore, ya ce a shirye kasarsa take, ta hada hannu da Singapore don aikewa da sakon da zai nuna batun kiyaye tsarin kasancewar bangarori da dama da yaki da ra'ayi na kashin kai da kariyar cinikayya.

Wang Yi ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da takwaransa na Singapore Vivian Balakrishnan, gabanin taron ministocin harkokin wajen Sin da na kasashe mambobin kungiyar kasashen kudu maso yammacin Asia da kuma makamancinsa na kasashen gabashin Asia.

A nasa bangaren, Vivian Balakrishnan ya amince cewa ya kamata kasashen biyu su tashi su yaki kariyar cinikayya da ra'ayi na kashin kai tare da inganta tsarin kasancewar bangarori da dama da ciniki cikin 'yanci da kuma dunkulewar tattalin arzikin yanki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China