in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in gwamnatin Sin ya gana da jami'in gamayyar larabawa da ministan wajen Masar
2018-07-09 12:25:10 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da babban sakataren kungiyar gamayyar kasashen larabawa (AL), Ahmed Aboul-Gheit, da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry a jiya Lahadi.

Aboul-Gheit da Shoukry sun kawo ziyara ne don halartar taron ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa wato (CASCF) karo na 8, wanda za'a gudanar a ranar 10 ga watan Yulin wannan shekara.

A yayin ganawa da Aboul-Gheit, Wang ya bukaci kasashen Sin da na gamayyar kasashen larabawa dasu kara zurfafa hadin gwiwarsu, kana su cigaba da tallafawa junansu game da manyan batutuwan da suka shafi moriyar bangarorin biyu, kuma su yi kokarin sauke nauyin dake wuyansu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya.

Aboul-Gheit yace kasashen Larabawa a shirye suke su kara yin hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", ya kara da cewa, yana fatan taron ministocin karo na 8 na CASCF wanda za'a gudanar zai haifar da kyakkyawan sakamako.

A zantawarsa da ministan harkokin wajen Masar, Wang ya bukaci bangarorin biyu dasu tabbatar da mutunta kyakkyawar alakar dake tsakaninsu, kana shugabannin bangarorin biyu su gudanar da cikakken jagorancin da zai kara ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba. jami'in na Masar ya yabawa kasar Sin a bisa kokarinta na hangen nesa don tabbatar bunkasar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya da kuma cigaban nahiyar Afrika, Shoukry yace kasarsa a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da hadin gwiwar CASCF, da kuma dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China