in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron baje koli mai taken "Ci gaban aikin kare hakkin dan Adam a Sin" a birnin Geneva
2018-09-11 11:04:27 cri

Jiya Litinin, an bude bikin baje koli mai taken "Ci gaban aikin kare hakkin dan Adam a Sin, bisa kwaskwarima da bude kofa ga waje da kasar ta yi". An gudanar da bikin ne a hedkwatar MDD dake birnin Geneva.

An kira wannan taro ne dai bisa hadin gwiwar ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasa ta Sin, da tawagar zaunannun wakilan kasar Sin dake MDD a birnin Geneva. Inda aka nuna hotuna kimanin guda 90 da wasu bidiyon da suka nuna game da sakamakon da kasar Sin ta cimma, wajen taimakawa masu fama da talauci.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva, kana wakilin sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland Yu Jianhua, da kuma shugaban sashen kula da harkokin hakkin dan Adam na ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasa ta Sin Li Xiaojun sun halarci bikin budewar taron, inda suka kuma ba da jawabi.

Cikin jawabinsa, jakada Yu Jianhua ya bayyana cewa, ya kamata a kare hakkin ko wane dan Adama, wannan shi ne babban burin gwamnati da al'ummar kasa ta Sin. Ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta sami ci gaba na a zo a gani a wannan fanni, musamman ma a fannin neman bunkasuwar aikin kare hakkin dan Adam bisa tsarin gurguzun musamman na kasar.

Shugaban kwamitin hakkin dan Adam na MDD Vojislav Suc, da babban sakataren kungiyar lura da 'yan ci rana ta kasa da kasa William Lacy Swing, da jakadun kungiyar EU, da na kasashen Burtaniya, da Jamus da dai sauran kasashe kimanin 30, da tawagogin zaunannun wakilan kasa da kasa dake birnin Geneva, da kuma wakilan hukumomin MDD da na kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda bisa jimilla suka haura mutane 600 sun halarci wannan taro. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China