in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ce ya kamata tattaunawa kan hakkin dan Adan ta zama mai ma'ana
2017-09-16 12:38:38 cri
Kasar Sin ta ce ya kamata kasashen duniya su rika gudanar da tattaunawa mai ma'ana tare da yin hadin gwiwa a fannin kare hakkin dan Adam.

Da yake jawabi yayin taro na 36 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, kasar Sin ta ce ya kamata al'ummomin kasa da kasa su yi aiki tare, sannan su kauracewa nuna yatsa da nuna karfi da wulakanci da sanya siyasa idan ana maganar batutuwan da suka shafi kare hakkin dan Adam.

Ma Zhaoxu shugaban tawagar wakilan kasar Sin a MDD dake Geneva, ya ce idan ana batun kare hakkin dan Adam, to akwai bukatar kasashe su rika daukaka manufofi da ka'idojin MDD.

Ya ce hakan na nufin kasashe su rika mutunta ikon mallakar yankin kasa da kuma hanyar samun ci gaba da tsarin zaman takewa da al'ummominsu suka zaba.

Na biyu shi ne, a rika tattaunawa tare da musayar bayanai. Inda ya kara da cewa, kasashe su mutunta tare da nuna daidaito ga juna, sannan su fadada fahimtarsu tare da rage sabanin dake tsakaninsu ta yadda za su hada hannu wajen inganta kare hakkin dan Adam. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China