Kuma babban taken muhawarar shi ne yadda aka aiwatar da sanarwar Durban da kuma ka'idojin gudanarwa, watau DDPA.
A yayin taron, wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, sanarwar DDPA tana da muhimmiyar ma'ana ga kasashen duniya wajen yaki da wariyar launin fata da sauran abubuwa masu nasaba da gajen hakuri. A halin yanzu, ana ci gaba da fuskantar mummunar nuna wariyar launin fata a wasu kasashen duniya, lamarin da ya haddasa kiyayya a tsakanin kabilu daban daban, da kuma tabarbarewar yanayin zaman rayuwar 'yan gudun hijira, inda a wasu lokutan aka kai wa wasu kanannan kabilu hare-hare da ba su kamata ba.
Bugu da kari, wakilai masu halartar muhawarar sun yi kira da a aiwatar da sanarwar DDPA yadda ya kamata, domin za ta taimaka wajen warware kalubalolin dake shafar wariyar launin fata da kuma nuna kiyayya ga baki dai sauran aikace-aikace masu nasaba da rashin hakuri da juna. (Maryam)