Wannan kuma shi ne karo na farko, da kwamitin kare hakkin dan Adama na MDD ya zartas da wani kudurin da ya shafi harkokin neman ci gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa, kudurin ya samu amincewar kasashe sama da 70.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin Geneva na MDD Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, wannan kuduri shi ne babbar gudummawa da kasar Sin ta samar wa kasa da kasa wajen gudanar da ayyukan kare hakkin dan Adam, kuma tabbas, zai kyautata matsayin kasashe masu tasowa kan wannan harka, yayin ciyar da ayyukan kare hakkin dan Adam na kasa da kasa gaba, cikin himma da kwazo. (Maryam)