in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Akwai kuskure cikin rahoton hakkin dan Adam da Sweden ta fitar
2017-05-02 19:59:57 cri
A kwanakin baya ne gwamnatin kasar Sweden ta fidda wani rahoto game da hakkin dan Adam, wanda a cikin sa aka yi suka kan yanayin kare hakkin dan Adam a kasar Sin.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya nuna rashin amincewa da hakan, a gun taron manema labaru da aka gudanar a nan birnin Beijing a yau Talata.

Mr. Geng Shuang ya bayyanawa 'yan jarida cewa, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan tabbatar da kare hakkin dan Adam. A cikin shekaru fiye da 30 bayan da kasar ta bude kofa ga kasashen waje, da fara aiwatar da kwaskwarima, an samu babbar nasara game da sha'anin tabbatar da hakkin dan Adam a kasar Sin, kuma wannan batu a fili yake kowa ya iya gani.

Ya ce Sin tana ganin cewa ya dace kasashen duniya su yi musayar ra'ayoyi kan batun kare hakkin dan Adam bisa tushen daidaito, da girmamawa juna, domin cimma nasarar koyi da juna, da samun ci gaba tare, kuma bai kamata a yi amfani da batun hakkin dan Adam, a matsayin hanyar tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China