A cikin jawabinsa, Yu Jianhua ya gabatar da manufofi guda hudu da suka hada da: na farko, a nemi ci gaban kasa da kasa ta yadda za a bada gudummawa kan aikin kare hakkin dan Adam, domin ci gaba shi ne mabudi na warware dukkan matsalolin da abin ya shafa. Shi ya sa, ya kamata a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen cigaba nan da shekarar 2030 da MDD ta tsara, domin kawar da talauci mai tsanani a duk fadin duniya.
Na biyu shi ne, ya kamata a kare tsaron kasa da kasa domin inganta harkokin kare hakkin dan Adam, domin yake-yake da tashe-tashen hankula su kan haddasa keta hakkin dan Adam.
Na uku kuma, ya kamata a ciyar da aikin kare hakkin dan Adam gaba ta hanyar yin hadin gwiwa.
A karshe ya ce, ya kamata a karfafa yanayin adalci wajen ciyar da aikin gaba. A halin yanzu, yawan mutanen kasashe masu tasowa ya kai kashi 80 bisa dari a duk fadin duniya, ya dace a kyautata matsayinsu kan wannan al'amari wajen nuna bukatunsu da kuma shawarwarinsu.
Bisa labarin da aka samu, an ce, an bude taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD karo na 37 a birnin Geneva a ranar 26 ga watan Fabrairu, kuma za a kawo karshen taron a ranar 23 ga watan Maris. (Maryam)