in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar zartarwar AU
2018-09-05 15:13:58 cri

Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU Moussa Faki a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan matakan kungiyar AU na dunkulewar kasashen Afirka, da kuma ba da karin gudummawa cikin harkokin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da kuma ayyukan taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. Cikin 'yan shekarun nan, an sami sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar AU, kana, bangarorin biyu sun cimma nasarar karfafa mu'amalar dake tsakaninsu kan harkokin kasa da kasa. Kuma a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa mu'amalarta da kungiyar AU kan manyan tsare-tsare, da karfafa hadin gwiwar tsakanin bangarorin biyu ta yadda za su aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare, da inganta hadin gwiwar Sin da AU kan ayyukan kiyaye tsaro da dai sauransu.

A nasa bangare, Moussa Faki ya bayyana cewa, "manyan matakai guda 8" da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya gabatar za su taimaka wa kungiyar AU wajen cimma ajadar raya nahiyar nan da shekarar 2063, da ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasashen Afirka. Kungiyar AU tana fatan hada kai da kasar Sin da ma sauran kasashe mambobin taron FOCAC wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC na birnin Beijing, ta yadda zai amfanawa al'ummomin Sin da Afirka baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China