in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Xi ya gana da takwaransa na Kenya
2018-09-05 10:06:25 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a jiya Talata, da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta, wanda ke halartar taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika.

Shugaba Xi Jinping, ya ce a shirye kasar Sin take ta karfafa hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu da yayata gogewarta a fannin shugabanci ga Kenya, da fadada hadin gwiwa a fannonin da suka shafi aikin gona da ginin ababen more rayuwa da kiwon lafiya da bunkasa ayyukan masana'antu da inganta mu'amala tsakanin al'ummominsu tare da taimakawa kasar wajen cimma manyan manufofinta 4.

Ya ce, kasar Sin na maraba da Kenya ta shiga shawarar ziri daya da hanya daya, kuma za ta mara wa kasar baya wajen gina yankin kasuwanci da na masana'antu a kusa da layukan dogo.

A nasa bangaren, shugaba Kenyatta, ya ce taron ya tsara alkiblar dandalin hadin gwiwa cikin shekaru masu zuwa, kuma zai inganta ci gaba na bai daya a Afrika da kasar Sin.

Ya ce, Kenya ta shiryawa zurfafa alakar dake tsakaninta da kasar Sin da kuma shiga cikin shawarar ziri daya da hanya daya da inganta cudanyar dake tsakaninta da kasar Sin. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China