in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Muhammadu Buhari
2018-09-05 13:40:41 cri

Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya jaddada cewa, Nijeriya wata babbar kasa ce a nahiyar Afirka, kuma muhimmiyar abokiya ta kasar Sin a nahiyar Afirka, Sin tana mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantaka tsakaninta da Nijeriya. Kaza lika, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta kasance dangantaka mafi kyau a tarihin kasashen biyu. Ya ce Sin tana matukar yabawa goyon bayan Nijeriya ga Sin, game da manufar kasar Sin daya tak, kuma tana fatan ci gaba da nuna fahimtar juna, da goyon baya, kan harkokin dake janyo hankulan kasashen biyu.

Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana maraba ga kasar Nijeriya da ta halartar aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Har ila yau tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, a fannonin gina ababen more rayuwa, da inganta ayyukan gona, da makamashi da dai sauransu, domin ba da taimako ga Nijeriyar wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, ta yadda hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, zai kasance abun koyi a fannin hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangare, shugaba Buhari ya bayyana cewa, taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, zai samar wa al'ummomin Sin da na Afirka wata makoma mai haske, kasancewarsa muhimmin dandalin hadin gwiwa. Ya ce, Nijeriya za ta yi hadin gwiwa da sauran mambobin FOCAC, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin din birnin Beijing. Haka kuma, kasar Nijeriya tana matukar yabuwa shawarar "Ziri daya da hanya daya", domin za ta kasance tushe mai karfi ga bunkasuwar kasar Sin da kasashen Afirka cikin hadin gwiwa. Nijeriya tana fatan shiga a dama da ita a wannan shawara tare da sauran kasashen da abun ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China