Akinwumi Adesina ya ce, cikin shekarun baya bayan nan, yawan bashin dake cikin ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasashen Afirka ya dan karu kadan, kuma adadin ya kai kashi 22 bisa dari a shekarar 2010, wanda ya karu zuwa kashi 37 bisa dari a shekarar 2017. Amma adadin bai kai kashi 100 bisa dari, ko kashi 150 bisa dari, kamar yadda kasashe masu ci gaba suke ba. Kana bai kai kashi 50 bisa dari na wasu kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki ba.
A yayin da yake tsokaci kan batun cewa wai "kasar Sin tana kara matsa wa kasashen Afirka lamba ta hanyar ba su bashi", Akinwumi Adesina ya jaddada cewa, bisa halin da kasashen Afirka suke ciki a yanzu, wato ana samun karuwar tattalin arziki cikin yanayin zaman karko, da kuma karuwar yawan al'umma, kasashen Afirka suna bukatar taimako na kyautata ababen more rayuwarsu, don haka suke samun bashi bisa bukatunsu na neman jari, a maimakon sayen kayayyaki. (Maryam)