in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana a Nijeriya sun bukaci gwamnatin kasar ta inganta dangantakar al'adu da Sin
2018-09-05 09:50:27 cri

Masana a Nijeriya, sun bukaci gwamnatin kasar ta inganta dangantakar al'adu da kasar Sin, bisa amfani da damarmakin dake tattare da taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika na bana.

Yayin wani taron karawa juna sani da ya gudana a ranar Litinin a Abuja, babban birnin kasar, domin tattauna manufofin taron FOCAC, masanan sun ce, a matsayinsu na hanyoyin tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummu, al'adu da yawon bude ido na da muhimmiyar rawar takawa wajen aiwatar da manyan shirye-shirye 8 da kasar Sin ta sanar tare da kasashen Afrika.

A cewar Otunba Olusegun Runsewe, shugaban hukumar kula da al'adu ta Nijeriya, akwai bukatar kasar ta karfafa danganta ta fuskar al'adu da yawon bude ido da kasar Sin, karkashin shirin da ya shafi mu'amala tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Shi kuwa Mohammed Suleiman, shugaban kungiyar tsoffin daliban kasar Sin a Nijeriya da a yanzu ke da mambobi sama da 5,000, cewa ya yi, kasar Sin da Nijeriya za su iya bunkasa alakarsu ta fuskar fadada mu'amala tsakanin al'ummominsu domin samun ci gaba ta hanyar musayar al'adu da shirye shirye na hadaka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China