180905-ministan-wajen-Nijar.m4a
|
A ranar 3 da 4 ga watan nan da muke ciki ne, aka kira taron kolin FOCAC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Babban taken taron shi ne "Yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, hada kanmu domin karfafa dunkulewar kasashen Sin da Afirka". Cikin zantawarsa da wakilin sashen Hausa na CRI, ministan harkokin wajen kasar Nijar Kalla Hankourao wanda ya zo birnin Beijing domin halartar taron ya bayyana cewa, batun karfafa dunkulewar kasashen Sin da Afirka cikin hadin gwiwa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ambata a yayin bikin bude taron, yana da muhimmiyar ma'ana, kuma tabbas zai ciyar da bunkasuwar kasashen Sin da Afirka gaba. (Maryam)