in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gana da shugaban Rwanda
2018-09-05 09:29:16 cri

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame, wanda ya halarci taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na wannan shekara da ya gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana taron kolin da aka kammala a matsayin mai muhimmanci a tarihi. Ya kuma bayyana godiyarsa ga Kagame wanda har ila shi ne shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka na wannan karo saboda halartar taron, da ma gudummawarsa ga samun nasarar shirya taron.

Xi ya ce, kamata ya yi sassan biyu su zurfafa tattaunawa da ci gaba da nuna wa juna goyon baya, da raya shawarar ziri daya da hanya daya da karfafa musayar al'ummu, ta yadda za a karfafa hadin gwiwar abokantaka.

A nasa jawabin, shugaba Kagame ya ce, nasarar taron kolin FOCAC na Beijing ta kara zurfafa alakar Sin da kasashen Afirka. Ya kuma godewa shugaba Xi na kasar Sin saboda muhimmancin da ya dora kan kasashen Afirka gami da gagarumar rawar da ya ke takawa wajen kara bunkasa alaka tsakanin Sin da Afirka.

Ya ce, bisa la'akari da abubuwan tarihi iri daya da kasashen biyu ke da shi, ya sa Afirka da Sin ke da kyakkyawan tushe na hadin gwiwar dake tsakaninsu. Ya kuma godewa kasar Sin kan taimakon da ta dade tana baiwa kasarsa. Yana mai cewa, Rwanda za ta ci gaba da bunkasa alakar dake tsakanin Sin da Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China