Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba
"Dalilin da ya sa huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta samu ci gaba lami lafiya shi ne domin sassan biyu sun nuna sahihanci a kai, haka kuma suna nunawa juna mutunci da biyayya. Har kullum kasar Sin tana cika alkawarin da ta yi. Na ji an ce, 'kara kula da Sinawan dake kasashen Afirka', ina tsammani babu bukata a yi haka, mu 'yan asalin kasashen Afirka muna da hankali, mun san abin da muke bukata, muna kokarin samun moriyarmu tare da abokan arzikin kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne kasar Sin da kasashen Afirka muna iya samun moriya tare."