Daga yau Litinin 3 zuwa gobe Talata 4 ga wata ne za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka FOCAC a nan beijing Beijing, bisa taken "Hadin gwiwa don moriyar juna, a kokarin raya makomar Sin da Afirka ta bai daya". Game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasashen Afirka dake halartar taron sun bayyana kamar hakan:
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob:
"Manyan ayyukan more rayuwa na kasashen Afirka na bunkasa sosai bisa taimakon kasar Sin. Kasar Sin ta zuba jari ga Afirka ne bisa bukatun kasashen Afirka amma ba tare da gindaya wani sharadi ba. Hadin kai a tsakanin bangarorin biyu suna gudana daidai wa daida, babu wanda ke dogaro bisa wani."