in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan taron FOCAC zai taimakawa Kenya wajen cimma "Manyan burika guda hudu", in ji babban sakataren jam'iyyar mulkin kasar Kenya
2018-08-26 16:53:02 cri
Kwanan baya, babban sakataren jam'iyya mai mulkin kasa ta Jubilee ta Kenya Raphael Tuju ya bayyana cewa, ana fatan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da za a yi a birnin Beijing zai ba da taimako ga kasar Kenya wajen cimma "Manyan burika guda hudu".

Raphael Tuju ya ce, muna mai da hankali sosai kan "Manyan burika guda hudu" da shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya fidda, kamar batun karancin abinci, muna fatan kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin da kasar Kenya za su iya yin hadin gwiwa kan wannan aiki. A sa'i daya kuma, ina sa ran kara hadin gwiwa da kasar Sin kan harkokin kirkire-kirkire. Kafa masana'antu a kasar Kenya zai ba da gudummawa ga kasar wajen daga matsayinta zuwa cibiyar kirkire-kirkire ta gabashin Afirka, zai kuma samar da karin guraben ayyukan yi ga matasan kasar.

A fannin gine-gine kuma, a matsayin wata kasa mai yawan al'umma, kasar Sin tana da fasahohi na zamani da kuma masu araha da dama wajen gudanar da ayyukan, ya kamata kasar Kenya ta yi koyo daga kasar Sin a wannan fanni.

A watan Disamba na shekarar 2017, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya fidda "Manyan buriku guda hudu" a ranar tunawa da 'yancin kai ta kasar Kenya, inda ya mai da hankali kan batutuwan dake shafar bunkasuwar zaman takewar al'ummar kasar, wadanda suka hada da tabbatar da samun isasshen abinci, raya harkokin kirkire-kirkire, gina gidaje masu araha da kuma ba da hidimar kiwon lafiya.

Haka kuma, Raphael Tuju ya ba da misali na layin dogon dake tsakanin tashar jirgin ruwa ta Mombasa da birnin Nairobi da kasar Sin ta ba da taimako wajen ginawa, ya ce, shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta fidda, ya samar da damammaki masu kyau ga kasar Kenya da ma sauran kasashen Afirka wajen neman ci gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China