in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Masar: Taron koli na FOCAC zai hade tsare-tsaren bunkasa Sin da Afrika wuri guda
2018-08-24 10:54:22 cri

Za a kira taron koli na Beijing, na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na FOCAC daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumba mai zuwa. A ran 23 ga wata, jakadan Sin dake Masar Song Aiguo ya zanta da manema labarai a birnin Alkahira, inda ya bayyana cewa, yayin taron, shugabannin Sin da Afrika za su gabatar da sabbin tsare-tsare da manufofi don kara hadin kansu, ta yadda za a ba da jagoranci a siyasance da samar da zarafi mai kyau ga zurfafa hadin kan Sin da Afrika a sabon zamani.

Babban taken taro a wannan karo shi ne "Hadin kai da samun muradu tare, don kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga jama'ar Sin da Afrika", babban aikin taro shi ne, hada tsare-tsaren Sin da Afrika tare, wajen samun bunkasuwa. Song Aiguo ya nuna cewa, a matsayinsu na kasa mai tasowa mafi girma da nahiya dake kunshi da kasashe masu tasowa mafi yawa, Sin da Afrika na da bukatu iri daya.

Song Aiguo na ganin cewa, babban aiki na biyu na wannan taro shi ne, hada hadin gwiwar Sin da Afrika da shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare. Ya ce, shawarar da aka gabatar shekaru 5 da suka gabata, ta zama wani mataki mai alfanu da Sin ta gabatarwa al'ummar kasa da kasa, wadda ta bayyana nauyin dake wuyanta, kuma ta samu karbuwa sosai daga kasashe dake da nasaba da ita, kasashen Afrika da dama na bayyana fatansu na shiga wannan babban aiki. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China