in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakada: Taron kolin FOCAC zai daga matsayin alakar Sin da Afirka
2018-08-24 11:44:19 cri
Jakadan kasar Sin dake kasar Habasha Tan Jian, ya bayyana cewa, ana saran taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka dake tafe, zai bullo da sabbin hanyoyin da za su kara daga matsayin alakar Sin da kasashen Afirka.

Da yake yiwa manema labarai karin haske kan taron kolin na FOCAC da zai gudana daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumban wannan shekara a birnin Bejing na kasar Sin, bisa taken," Sin da Afirka, karfafa al'umma mai kyakkyawar makoma ta hanyar hadin gwiwar moriyar juna", Jakada Tan Jian ya ce taron kolin zai kasance na tarihi da zai hallara iyalai daga bangaren Sin da kasashen Afirka, bayan makamancinsa da ya gudana a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.

Jakadan na Sin ya ce taron kolin na Beijing zai sake yin kira ga Sin da Afirka da su karfafa al'umma mai kyakkyawar makoma a nan gaba. Ya ce, ta wannan taron kolin, kasar Sin za ta hade shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya" da ajandar raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063 da kungiyar tarayyar Afirka ta gabatar, da ajadar MDD na samun dawamammen ci gaba nan da shekarar 2020 da kuma matakan raya kasashen Afirka daban-daban.

Ya kuma bayyana cewa, ana saran shugabannin kasashen Afirka da dama da shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka da babban sakataren MDD, da kungiyoyin kasa da kasa na shiyyoyin Afirka kimanin 27 ne za su halarci taron kolin.

Ita ma yayin zantarwarta da kamfanimn dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan kwamishiniyar kungiyar tarayyar Afirka mai kula da walwalar jama'a Amira Elfadil, ta ce taron kolin na FOCAC, taron koli ne da Sin da kasashen Afirka suka saba yi a tsakaninsu, kuma dukkan sassan biyu sun kintsa yadda ya kamata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China