in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Habasha: Taron kolin FOCAC zai mayar da hankali kan noma, kamfanoni, kayan more rayuwa, kimiyya da fasaha
2018-08-26 15:35:17 cri
Jiya Asabar wani jami'in kasar Habasha ya bayyana cewa taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC) dake tafe wanda za'a gudanar a Beijing, ana sa ran zai mayar da hankali kan sauye-sauye a fannin aikin gona, bunkasa masana'antu, bunkasa samar da kayayyakin more rayuwa da kuma bunkasa fannin kimiyya da fasaha.

A wata cikakkiyar hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Admasu Nebebe, mataimakin ministan kudi da tattalin arzikin kasar Habasha, ya ce taron kolin na FOCAC ana sa ran zai tattauna game da yadda kasar Sin da kasashen Afrika za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu musamman a wadannan muhimman bangarori guda 4.

"Kasashen Afrika suna bukatar sauya fasalin fannin aikin gona, suna bunkasa ci gaban masana'antu, da zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa da kuma fannin ci gaban kimiyya da fasaha muddin suna son cimma burinsu na samun bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda kasar Sin ta samu," in ji Nebebe.

Nebebe ya kara da cewa, dangantakar Sin da Afrika kuma musamman dangantakar Sin da Habasha, ya kunshi batun samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da hadin gwiwa kan ilmi a matsayin jigo, yayin da 'yan kasar Habasha kusan mutane 6,000 ne suke samun ilmi daga kasar Sin a cikin shekaru masu yawa da suka gabata, kuma akwai karin daruruwan 'yan kasar Habashan dake shirye-shiryen halartar manyan makarantun kasar Sin don samun ilmin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China