in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Gabon dake Sin: Taron kolin dandalin FOCAC zai habaka hadin gwiwar Sin da Afirka
2018-08-23 18:39:46 cri

Za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Satumba dake tafe a nan birnin Beijing, yayin taron, shugabannin sassan biyu za su taru gu daya domin tattauna kan hadin gwiwar dake tsakaninsu a sabon zamanin da ake ciki.

Jiya Laraba, jakadan kasar Gabon dake wakilci a nan kasar Sin Baudelaire Ndong Ella ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ya zama abin koyi ga kasashe masu tasowa, yayin da suke gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu. Kuma ya dace sassan biyu su ci gaba da kara karfafa cudanya, tare kuma da taka rawar gani a harkokin kasa da kasa, yana sa ran cewa, taron kolin dake tafe zai samu cikakkiyar nasara.

Jakadan ya yi nuni da cewa, tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya kafin shekaru biyar da suka gabata, kasashen da suka shiga shawarar sun ci babbar gajiya daga hakan. Ya ce Gabon tana ganin cewa, shawarar tana da babbar ma'ana, ta yadda za ta bude wani sabon shafi ga ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China