in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Beijing ta shirya karbar bakuncin taron kolin dandalin FOCAC
2018-08-22 18:53:29 cri

Za a kira taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2018, a tsakanin ranekun 3 zuwa 4 ga watan Satumba mai zuwa a nan birnin Beijing, inda shugabannin kasashen Sin da na Afirka, za su gana da juna domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu.

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, taron kolin da za a gudanar, taro ne mafi muhimmanci da kasar Sin za ta karbi bakuncin sa, wanda zai samu halartar shugabannin kasashen ketare mafiya yawa a shekarar da muke ciki. Ya kara da cewa, birnin Beijing ya shirya karbon bakuncin taron, zai kuma taryi aminai daga kasashen Afirka, wadanda ke goyon bayan al'ummar kasar Sin a ko da yaushe.

Jami'in ya bayyana cewa, yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da wani muhimmin rahoto, inda zai yi cikakken bayani kan sabbin manufofin da gwamnatin kasar Sin za ta aiwatar, da sabbin matakan da za ta dauka, domin kara kyautata huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, musamman ma a fannonin raya sha'anin samar da kayayyaki, da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da cinikayya da zuba jari, da horas da ma'aikata, da ci gaban kimiyya da ba da ilmi da al'adu da kiwon lafiya, da kiyaye muhalli, da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dai sauransu.

Duk wadannan sabbin matakan da kasar Sin za ta dauka, za su biya bukatun bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka, haka kuma za su ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata, tare kuma da taka muhimiyyar rawa a fannin ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Afirka, bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China