Meles Alem ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da wakilinmu, ya kuma nuna yabo sosai kan tallafin da Sin ta dade tana baiwa kasashen Afirka, a cewarsa hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka hadin kai ne na na zaman daidai wa daida da samun moriyar juna, kasar Sin tana girmama 'yancin kasashen Afirka a fannin siyasa, kuma tana tallafawa kasashen Afirka ba tare da gindaya wasu sharuda ba.
Ban da wannan kuma, kasar Sin ita ce ta biyu a fannin tattalin arziki a duniya, hakan zai taimaka matuka ga ci gaban Afirka.
Baya ga haka, Meles Alem ya bayyana cewa, shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar na da amfani wajen karfafa hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ayyukan zuba jari da Sin ke yi kan manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kasashen Afirka na da ma'ana kwarai ga ci gabansu, kana kuma ba za a iya raba taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka ba wajen gudanar da ayyukan manyan kayayyakin more rayuwa. Ya zuwa yanzu, yawan jarin da Sin ta zuba a Habasha ya kai dala biliyan 4, Sin ta kuma nuna goyon baya ga Habasha a fannonin fasaha da kudi, don raya manyan kayayyakin more rayuwa da aikin samar da makamashi. (Bilkisu)