Bugu da kari, ma'aikatar ta kafa wani kwamitin musamman ne da ya gudanar da bincike kan ko sauran fursunonin sun cika sharadin a yafe musu laifi, ko a'a. A karshe kuma, ya tabbatar da cewa mutane 1749 ne suka cika sharadin.
Rahotanni na cewa, shugaban kasar Masar ya kan yi ahuwa ga fursunoni a lokacin da ake gudanar da wasu manyan bukukuwa. (Maryam)