in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da Abdel Fatah al Sisi a matsayin shugaban kasar Masar a wa'adi na 2
2018-06-03 16:03:05 cri
An rantsar da Abdel Fattah al-Sisi jiya a Asabar, a matsayin Shugaban kasar Masar a wa'adi na 2 da zai kai shekarar 2022.

Gidan talabijin na kasar na Nile, ya ruwaito cewa, yayin wani gagarumin biki da ya gudana a majalisar dokokin kasar, Shugaba Sisi ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa. Inda ya rantse zai kare tsarin Jamhuriya na kasar da girmama kundin tsarin mulkin kasa da kare muradun jama'a da kiyaye 'yancin kan kasar da hadin kan yankunanta.

Jiragen yakin Masar da jirage maso saukar ungulu ne suka yi wa jerin gwanon motocin tsohon kwamnadan sojin rakiya zuwa hedkwatar majalisar dokokin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China