in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun jikkata sanadiyyar fashewar tankokin mai a Masar
2018-07-13 09:29:01 cri
Mutane 12 sun jikkata sanadiyyar fashewar wasu tankokin mai a kusa da filin jirgin saman Cairo, babban birnin Masar, a daren ranar Alhamis, sai dai al'amarin bai shafi sufurin jiragen sama ba.

Jami'an tsaro sun shaidawa kamfanin dallancin labarai na kasar wato MENA cewa, al'amarin ya auku ne a yankin Heliopolis na Cairo.

Sanarwar da ministan sufurin jiragen sama na kasar, Mohamed Younis al-Masri ya fitar, ta ce wasu tankoki biyu mallakar wani kamfanin mai ne suka fashe a kusa da filin jirgin saman birnin Cairo.

Ya ce dukkan jirage na ciki da wajen kasar na zirga-zirga kamar yadda suka saba.

Ya kara da cewa, fashewar ta auku ne saboda zafi da ya yi yawa, kuma an yi nasarar takaita gobarar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China