Kotun ta kuma yankewa tsohon minista a fambararriyar gwamnatin Mohamed Morsi, wato Bassem Ouda, hukuncin daurin shekaru 15, yayin da ta kuma zartas da hukuncin daurin shekaru 10 ga wasu mutane su 3. To sai dai kuma ana iya daukaka kara game da wannan hukunci.
Hukuncin ya biyo baya na shari'ar da aka sabunta kan mutanen, bayan da a watan Satumba na shekarar 2014, kotun ta yankewa wasu magoya bayan kungiyar su 15 hukuncin daurin rai da rai.
A wani ci gaban kuma, wata kotun dake zaman ta a birnin Alkahira, ta mika takardun neman amincewar babban mai bada fatawa na kasar, game da yiwuwar zartas da hukuncin kisa kan wasu 'yan kungiyar su 3 da ake tsare da su, bayan da ta tabbatar da zargin da ake musu na kafa kungiya mai adawa da gwamnatin kasar ta Masar, da kuma goyon bayan ta'addanci. Ana dai sa ran kotun za ta bayyana hukuncin karshe kan mutanen su 3 a ranar 14 ga watan Oktoba dake tafe. (Saminu Hassan)