in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar: Sherif Ismail ya gabayar da takardar aje aiki
2018-06-06 13:30:33 cri

Firaministan kasar Masar Sherif Ismail, ya mika takardar murabus ga shugaban kasa Abdel-Fattah al-Sisi, matakin da ke alamta kawo karshen gwamnatin da ya jagoranta. Kakakin fadar shugaban kasar Bassam Rady ne ya sanar da hakan a jiya Talata.

Murabus din firaministan dai na zuwa ne, 'yan kwanaki kalilan da rantsar da shugaban na Masar a wa'adin aiki na biyu na shekaru 4, gaban mambobin majaliassar dokokin kasar.

Tuni dai shugaba Sisi ya mika ragamar gwamnatin ga wakilan rikon kwarya domin ci gaba da ayyukan hukuma, gabanin kafa sabuwar gwamnati nan da 'yan kwanaki.

Wata sanarwa da Bassam Rady ya fitar, ta ce murabus din wakilan gwamnatin kasar al'ada ce da tsarin mulkin kasar Masar ya gada, wadda kan wakana a duk lokacin da aka rantsar da sabon shugaban kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China